
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani kwamitin bincike na musamman da zai duba gobarar da ta tashi a kasuwar wayoyi ta Farm Centre.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya jagoranci kaddamarwar a madadin Gwamnan Kano, inda ya ce kwamitin zai binciki musabbabin gobarar da kuma yadda za a hana faruwar irin ta nan gaba.
Ya ce an nada kwamitin ne domin ya gano ainihin dalilan gobarar, ya tantance irin barnar da aka yi, da kuma bayar da shawarwari masu amfani da za su hana sake faruwar irin hakan.
Ya kuma ja kunnen ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji siyasantar da batun tallafi ga wadanda gobarar ta shafa. Ya ce dukkan gudummawa da tallafi ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa za a rika karbarsu ta hannun kwamitin ko kuma ta asusun bankin da gwamnati ta ware domin hakan kamar yanda sanarwar Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Ciki Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar
Shugaban Kwamitin shi ne Kwamishinan Aiyuka na Musamman na Jihar Kano, Alhaji Nasiru Sule Garo, kuma kwamitin ya kunshi wakilai daga hukumomin gwamnati, na tsaro, kungiyoyin ‘yan kasuwa, da masu zaman kansu.
Wasu daga cikin hukumomin da ke cikin kwamitin sun hada da Ma’aikatar Tsaro da Ayyuka na Musamman, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Ciki, SEMA, Rundunar ‘Yan Sanda, DSS, KNUPDA, KACCIMA da kuma kungiyar ‘yan kasuwar GSM na Farm Centre.
Sauran sun hada da wakilan kananan hukumomi, manyan jami’an gwamnati da masu bayar da shawara, inda Alhaji Abdulkadir Shehu AGS-HOC zai kasance Sakataren kwamitin.
AYYUKAN KWAMITIN SUN HADA DA:
1. Binciken musabbabin gobarar.
2. Kimanta barnar da ta auku da asarar rayuka idan akwai.
3. Duba yadda hukumomi suka mayar da martani lokacin aukuwar gobarar.
Advertisement
4. Tantance matakan kariya da ke kasuwar a halin yanzu.
5. Bayar da shawarwari don hana aukuwar gobara a gaba.
6. Tattaunawa da wadanda abin ya shafa da sauran shaidu.
Advertisement
7. Tattara sunaye da bayanan wadanda suka yi asara.
8. Nazarin tsarin gine-ginen kasuwar da tsaron muhalli.
9. Samar da shawarwari kan yadda za a tafiyar da kasuwar cikin tsari.
10. Karbar duk wata gudummawa cikin sahihin asusun gwamnati.
11. Mikawa gwamnati cikakken rahoto cikin mako guda daga ranar da aka kaddamar da kwamitin.
Gwamnatin Kano ta ce tana daukar wannan lamarin da matukar muhimmanci, kuma tana da niyyar sake gina kasuwar cikin tsari da kariya daga afkuwar gobara a gaba.
Ta kuma bukaci hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aikin kwamitin da kuma rage radadin da gobarar ta haifar.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2349024003431
thnaks you